Daga cikin wuraren kasuwanci da suka gurfana a gaban Kotun Tsaftar Muhalli ta REMASAB a zagayen dake gudanarwa duk sati na wannan makon akwai Domino’s Pizza, Jalsa Shop, Bankin FCMB da Nasarawa Suya Spot, wadanda duk suke kan titin Bompai Road.


Binciken da kotun ta gudanar ya gano laifukan da guraren suka aikata da suka haɗa da barin ciyayi da suka yi tsayi sosai, zubar da shara ba bisa ka’ida ba, rashin share yana da rashin isassun kwandunannan zubar da shara, da kuma gaza kula da muhalli yadda ya kamata.


Bisa dokokin tsaftar muhalli da ake aiki da su a yanzu, Kotun tafi da gidanka na hukumar Tsaftar Muhalli ta yanke wa waɗannan wurare hukuncin ɗaurin makonni biyu ko kuma biyan tara.


Manajan Daraktan REMASAB, Dr. Muhammad S. Khalil, ya yi kira ga al'umma musamman yan kasuwa, masu kamfanoni da sauran wuraren sana’a a faɗin jihar Kano da su ɗauki batun tsaftar muhalli da muhimmancin da ya dace, tare da tabbatar da cewa ana tsaftace wuraren kasuwanci da kuma kiyaye su cikin tsari a kowane lokaci.


Dr. Khalil ya kuma ƙarfafa gwiwar jama’a da su riƙa zubar da shara yadda ya kamata, samar da isassun kwandunan shara, share ciyayi da suka yi tsayi cikin gaggawa, tabbatar da cewa magudanan ruwa ba su toshe ba, da kuma kula da kayan aikin tsafta a cikin wurarensu yadda ya kamata.