Tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, a ranar Talata ya bayyana masana’antar kirkire - kirkire ta Najeriya a matsayin kafar samun kudin shiga na biyu mafi girma wato “man fetur na gaba” ga ƙasar, yana mai cewa ɓangaren na da babbar damar samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arziki.


Mohammed ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taro tsakanin shugabannin Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa (NIPSS) da Ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Kirkire- kirkire, Hannatu Musawa.


An gudanar da taron ne a wani ɓangare na ƙoƙarin NIPSS da ma’aikatar wajen samar da dabarun amfani da ɓangaren kirkire - kirkire domin tallafa wa manufar Shugaba Bola Tinubu ta bunƙasa tattalin arzikin Najeriya zuwa dala tiriliyan ɗaya ($1tn) nan da shekarar 2030.


Tsohon ministan, wanda shi ne Manajan Abokin Hulɗa na kamfanin tuntuba na Bruit Costaud, mai ba da shawara kan taron ƙasa da baje kolin Orange Economy da ke tafe, ya ce ya kamata Najeriya ta daina dogaro da ɗanyen mai kawai, ta kuma mayar da hankali wajen amfani da damar tattalin arziki da ke cikin masana’antun kirkire - kirkire da al’adunta.


Ya mai cewa “A lokacin da nake minista, na sha faɗa cewa man fetur ɗinmu na gaba shi ne masana’antar kirkire - kirkire— wato fina-finai, kiɗa, wasanni da sauran su.


“Muna kallon wannan ma’aikata a matsayin ɗaya daga cikin ma’aikatu mafi muhimmanci, domin bayan noma, ita ce ma’aikatar da ke ɗaukar mafi yawan ma’aikata.”


Mohammed ya ce kamfaninsa na matuƙar sha’awar haɗa gwiwa da NIPSS wajen shirya Taron Ƙasa da Baje Kolin Orange Economy, wanda ake sa ran zai haɗa manyan masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arzikin kere-kere na Najeriya.