Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Najeriya (NHRC) ta yi Allah-wadai da wasu kalaman malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir, tana mai cewa kalaman na iya ƙara rura wutar ƙiyayya da rarrabuwar kawuna tsakanin mabiya addinai a Najeriya.
Hukumar ta buƙaci Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, DSS da sauran hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace kan Sheikh Jingir bisa zargin furta kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a.
Shugaban NHRC, Tony Ojukwu, SAN, ya ce kalaman malamin da suka yaɗu a wani faifan bidiyo sun ƙunshi abin da hukumar ta bayyana a matsayin siyasar wariya ga wasu addinai, tare da amfani da kalmar “kafirai.”
A cewar Ojukwu, irin waɗannan kalamai na iya ƙara raunana fahimtar juna tsakanin al’ummomin addinai daban-daban tare da haifar da tashin hankali. NHRC ta daɗe tana gargadin cewa kalaman ƙiyayya na iya barazana ga zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da kuma sahihancin tsarin dimokuradiyya musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Hukumar ta kuma yi kira ga malaman addini, sarakuna, ’yan siyasa da sauran masu tasiri a cikin al’umma da su guji kalaman da za su iya raba kan jama’a ko tayar da ƙiyayya tsakanin addinai.
NHRC ta jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido, tattara bayanai da mayar da martani kan kalaman ƙiyayya da ka iya yin tasiri ga zaman lafiya da haƙƙin ɗan Adam a Najeriya yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.