Wata kotu a Syria ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Bashar al-Assad, hukuncin kisa ba tare da ya bayyana a gaban kotu ba, bayan ta same shi da laifukan yaƙi da cin zarafin bil’adama, ciki har da kisa, azabtarwa da kamawa ba bisa ƙa’ida ba.
Wannan shi ne hukunci na farko da aka yanke wa Assad tun bayan hambarar da gwamnatinsa a watan Disamban 2024. Bayan faduwar gwamnatin, Assad ya tsere daga Damascus zuwa Moscow tare da iyalansa, inda ya samu mafaka a Rasha.
Hukuncin ya shafi laifukan da ake zargin an aikata a lokacin yakin basasar Syria da ya ɗauki kusan shekaru 14, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan rabin miliyan na mutane.
Kanin Assad, Maher al-Assad, da kuma wasu tsoffin jami’an gwamnatin sa ma sun fuskanci hukuncin kisa, yayin da ɗan uwansu Atef Najib shi ne babban jami’in da aka gurfanar a gaban kotu da kansa.
Hukuncin na zuwa ne a matsayin wani muhimmin mataki na ƙoƙarin sabuwar gwamnatin Syria na neman ɗaukar matakin shari’a kan manyan jami’an tsohuwar gwamnatin Assad. Sai dai wasu masana shari’a sun nuna damuwa kan yadda aka gudanar da shari’ar da kuma yiwuwar hukuncin kisan ya kawo cikas ga ƙoƙarin ganin an gurfanar da Assad a gaban wata kotu ta ƙasa da ƙasa.