Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation ENDURING PEACE da ke aiki a Jihar Filato sun samu nasarar dakile wani kwanton bauna da ake zargin ’yan bindiga ne suka shirya a ƙaramar hukumar Langtang ta Arewa.

Rundunar ta ce sojojin sun kai samamen ne bisa sahihan bayanan sirri, inda suka kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne. Wanda ake zargin ya jagoranci jami’an tsaro zuwa ƙauyen Nwur, inda ya ce ya ɓoye makamansa.

Yayin da dakarun ke rakiyar wanda ake zargin zuwa wurin domin gano makaman, wasu daga cikin abokan aikinsa suka kai musu hari.

Sai dai sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, lamarin da ya yi sanadin kashe ɗaya daga cikin maharan.

Rundunar ta ce wanda aka kama tun farko shi ma ya mutu yayin musayar wutar da ta barke tsakanin ɓangarorin biyu.

Bayan kammala artabun, dakarun sun gudanar da bincike a yankin, inda suka ƙwato makamai, harsasai da sauran kayan yaƙi da maharan suka bari yayin da suke tserewa.

Rundunar ta ce dakarunta na ci gaba da gudanar da sintiri da farautar sauran masu aikata laifuka a yankin, tare da jaddada ƙudurinta na hana masu aikata laifuka samun mafaka da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.