Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta 10 a wani artabu da ’yan bindiga a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:25 na safiyar Litinin, 10 ga Agusta, 2026, a yankin Rafin Makuku, da ke ƙaramar hukumar Sakaba.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar na ƙasa, CSP Ani Iniedu, ya fitar, ya ce jami’an ’yan sandan sun tare wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai yayin da suke ƙoƙarin ratsa hanyar da ta haɗa jihar Zamfara da Kebbi.
Ya ce hakan ya haifar da musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da maharan.
Rundunar ta ce an kashe aƙalla ’yan bindiga 17, yayin da aka lalata babura huɗu da ake zargin maharan suka yi amfani da su.
Sai dai, jami’an ’yan sanda 10 sun rasa rayukansu a yayin artabun, yayin da wasu jami’ai biyu suka samu raunuka kuma suke karɓar magani.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa fararen hula biyu sun rasa rayukansu a yayin musayar wutar.
An ƙara tura jami’an tsaro zuwa yankin domin ci gaba da gudanar da ayyuka na musamman da kuma tabbatar da tsaron al’ummar yankin.