Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna, yana mai cewa haɗin kan ƙasa na da muhimmiyar rawa wajen tunkarar ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wani taron ƙasa da ƙasa kan Tsaron Ƙasa da Bunƙasar Tattalin Arziki da Jin Daɗin Al’umma mai ɗorewa, wanda aka gudanar a Abuja.
Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar Muslim League of Nigeria.
Mai Alfarma Sarkin ya jaddada cewa haɗin kan ’yan Najeriya yana da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Ya kuma bayyana cewa a wurin Allah, mafificin mutum shi ne wanda ya fi kowa tsoron Allah, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da tsoron Allah a matsayin ginshiƙi wajen taimakon juna, kyautata zamantakewa da ƙarfafa zaman lafiya a ƙasa.
Sarkin Musulmi ya buƙaci ’yan Najeriya su fifita abin da ya haɗa su a matsayin al’umma, tare da guje wa duk wani abu da zai iya haifar da rarrabuwar kai ko raunana haɗin kan ƙasa.