Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa tsaro a faɗin Najeriya da kuma bayar da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya ta hanyar haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ne ya bayyana hakan yayin da yake wakiltar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a taron ƙasa da ƙasa kan Tsaron Ƙasa da Bunƙasar Tattalin Arziki da Jin Daɗin Al’umma mai ɗorewa, wanda aka gudanar a Abuja.

Sanata Barau ya ce gwamnatin tarayya na yin duk mai yiwuwa wajen inganta tsaro a Najeriya, tare da haɗa kai da sauran ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa na da muhimmiyar rawa wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da kuma samar da yanayin da zai ba da damar samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa mai ɗorewa.