Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da cewa an kashe ’yan bindiga 17 da ake zargi a wata arangamar musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi.

Rundunar ta kuma ce wasu daga cikin jami’anta da fararen hula biyu sun rasa rayukansu yayin arangamar.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:25 na safiyar Litinin, a yankin Rafin Makuku na Sakaba, lokacin da jami’an ’yan sanda suka tare wasu da ake zargin ’yan bindiga ne yayin da suke ƙoƙarin ratsa yankin tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi.

Rundunar ta ce an kuma lalata babura huɗu da ake zargin maharan ne suka yi amfani da su.

Haka kuma, wasu jami’an ’yan sanda biyu sun samu raunuka kuma a halin yanzu suna karɓar magani.

An kai gawarwakin jami’an da suka mutu zuwa Birnin Kebbi, yayin da aka ƙara tura wasu jami’an tsaro zuwa yankin domin ci gaba da ayyukan dakile ayyukan ’yan bindiga da tabbatar da tsaron al’umma.