Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya yaba wa jami’an leƙen asiri da hukumomin tsaro bisa kama wasu mutane uku da ake zargi mambobin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane ce, wadda ake zargi da kai harin ranar 2 ga Agusta, 2026 a Cocin Katolika na St. Joseph da ke Inoyi-Affa, a ƙaramar hukumar Udi ta jihar.

An gudanar da samamen ne ta haɗin gwiwar Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Sojojin Najeriya, ’Yan Sanda, Enugu State Forest Guard da sauran jami’an tsaro.

A yayin arangamar da aka yi da waɗanda ake zargin masu garkuwar, an kashe wani daga cikin mambobin ƙungiyar, yayin da jami’an tsaron suka kwato bindigogi kirar AK-47 guda huɗu da kuma tarin harsasai.

Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Chidiebere Onyia, ya wakilta, ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai hedikwatar DSS ta jihar, domin ganawa da mutanen da aka kama.

A yayin ziyarar, an bayyana cewa biyu daga cikin mutane uku da aka yi garkuwa da su a harin na 2 ga Agusta, wato Seminarian Lawrence Igbo da Emmanuel Onwudi, sun samu ’yancinsu.

Sakataren gwamnatin jihar ya ce waɗanda aka sace sun gane mutanen da aka kama a matsayin waɗanda suka yi garkuwa da su.

A madadin gwamnan, SSG ya tabbatar wa al’ummar Enugu cewa gwamnatin Mbah za ta ci gaba da ba da fifiko da kuma zuba jari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da cewa waɗanda ake zargin za su fuskanci hukunci gwargwadon tanadin doka idan kotu ta same su da laifi.

Ya ce gwamnatin jihar ta fito fili ta bayyana cewa ba za ta lamunci aikata laifuka ba, yana mai cewa za a ci gaba da farautar masu aikata laifuka har sai an gurfanar da su a gaban doka.

SSG ya kuma gargadi jama’a da kada su haɗa kai da masu aikata laifuka ko kuma su riƙa ba su bayanan sirri, yana mai cewa duk wanda aka samu yana taimaka wa masu laifi zai fuskanci kama shi da gurfanar da shi.

Ya yaba wa jami’an tsaro bisa haɗin kai da jarumtakarsu, musamman DSS, Sojojin Najeriya, ’Yan Sanda, Enugu State Forest Guard da sauran hukumomin tsaro da suka taka rawa wajen gudanar da aikin.