Rundunar Sojin Najeriya ta buɗe damar neman aikin soja na Short Service na Shekarar 2027 ga fararen hula da jami’an soji masu aiki da suka cika sharudda.


Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar ɗaukar ma’aikata da ta fitar a ranar Talata, inda ta gayyaci ’yan Najeriya da suka cancanta da su nemi gurbin zama jami’an soja ta tsarin Short Service Combatant Commission.


A cewar sanarwar, waɗanda suka yi nasara za su yi aiki ne a ɓangaren Combat Arms, wanda ya haɗa da rundunonin Infantry da Armour, da kuma ɓangaren Combat Support Arms, wanda ya ƙunshi Artillery, Engineers, Signals da Intelligence Corps.


Rundunar Sojin ta ce damar neman aikin a buɗe take ga “fararen hula” da kuma “sojoji/ratings/airmen” da suka cika dukkan sharuddan da aka gindaya.