Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta saki wani kafinta mai suna Mustapha Marwana, bayan bincike ya tabbatar da cewa babu wata shaida da ke nuna yana da alaƙa da ayyukan ta’addanci.

Marwana, ɗan asalin jihar Katsina, an kama shi ne bisa zargin hannu a sacewa da kashe ɗaliban makaranta da malamai a ƙaramar hukumar Oriire da ke jihar Oyo.

Sai dai wani kwamitin bincike na DSS ya gano cewa babu wata shaida da ta danganta Marwana da kasancewa mamba, mai ɗaukar nauyin kuɗi, mai samar da kayan aiki ko kuma mai gudanar da ayyukan ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru.

Bayan kammala binciken, Darakta-Janar na DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, ya bayar da umarnin sakin Marwana nan take, tare da amincewa da biyan sa naira miliyan uku a matsayin tallafin farko domin taimaka masa wajen komawa rayuwar yau da kullum da kuma sake farfaɗo da sana’arsa.

An miƙa Marwana ga lauyansa, Oghene Forgive, bayan an sake shi.

Da yake magana bayan sakinsa, Marwana ya nuna godiyarsa ga shugabannin DSS bisa abin da ya bayyana a matsayin matakin tausayi da adalci da suka ɗauka.

DSS ta ce biyan diyya ga mutanen da bincike ya wanke daga zarge-zarge na daga cikin ƙoƙarinta na tallafa wa waɗanda aka tabbatar da cewa ba su da hannu a laifukan da aka zarge su da aikatawa, tare da ƙarfafa amincewar jama’a ga hukumar.

Hukumar ta ƙara da cewa a ƙarƙashin jagorancin yanzu, ta biya sama da naira miliyan 300 ga mutanen da aka wanke daga zarge-zarge ko kuma waɗanda aka kama sakamakon kuskuren gane mutum.