Gwamnatin Najeriya ta tura wata tawaga zuwa ƙasar Birtaniya domin rage wahalhalun da ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasar ke fuskanta wajen samun fasfo.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi, ta bayyana cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya jagoranci shirin a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na ci gaba da inganta ayyukan fasfo ga ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje.

Hukumar ta ce Ministan ya umarci Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) da ya tura jami’an hukumar zuwa Birtaniya domin rage matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta wajen samun fasfo.

A cewar hukumar, an shirya tawagar ta isa Birtaniya a ranar 10 ga Agusta, 2026, inda za ta yi aiki tare da Babban Ofishin Jakadancin Najeriya domin sauƙaƙa tsarin karɓar bayanai, sarrafawa da bayar da fasfo ga waɗanda ke jiran kammala nasu, da kuma masu neman sabbin fasfo ko sabunta tsofaffinsu.

Haka kuma, tawagar za ta ziyarci wasu zaɓaɓɓun birane a faɗin Birtaniya domin gudanar da ayyukan ɗaukar bayanai da sarrafa fasfo.

Hukumar ta ce hakan zai ba ’yan Najeriya da suka cika sharuddan neman fasfo a sassa daban-daban na Birtaniya damar samun damar yin amfani da ayyukan hukumar cikin sauƙi, ba tare da fuskantar dogayen tafiyoyi ko jinkiri ba.