Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce wasu kalaman malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir, na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Najeriya.

A wata sanarwa da Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana damuwarsa kan kalaman Sheikh Jingir da ya yi a wani taro a Kano a ƙarshen mako.

Kwankwaso ya jaddada cewa al’ummar Kano ba sa goyon bayan kalaman da za su iya raba kan ’yan Najeriya, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da murya ko matsayi wajen furta kalaman da za su raunana haɗin kan ƙasa ba.

A kwanakin baya ne kafafen sada zumunta da na yaɗa labarai suka ɗauki zafi sakamakon cece-kuce kan kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙungiyar Izala, dangane da batun Muslim-Muslim.

Kwankwaso, wanda shi ne mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce abin damuwa ne yadda irin waɗannan kalamai ke fitowa daga bakin malamin addini da ke da matsayi da tasiri a tsakanin al’umma.

Ya ce: “Bai kamata mu yi amfani da muryarmu wajen faɗin kalaman da za su iya raunana haɗin kan ƙasarmu ba.”

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa, a wannan lokaci da Najeriya ke ciki, ya kamata a yi watsi da duk wasu kalamai ko ayyukan da ka iya haifar da rashin haɗin kai tsakanin al’ummar ƙasar.