Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da ƙarin albashi ga malamai da sauran ma’aikatan jami’o’in jihar.
Ƙarin albashin zai shafi Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil da kuma Jami’ar Northwest.
Gwamnan ya amince da matakin ne bayan wani kwamiti da Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta kafa ya duba buƙatar jami’o’in biyu na shigar da sabon tsarin albashin cikin tsarin jihar.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin, sabon tsarin albashin ya fara aiki tun daga Janairun 2026, yayin da za a fara biyan ƙarin kuɗin daga Satumban 2026.
Sanarwar ta ce ƙarin albashin jami’o’in biyu zai ci wa gwamnatin jihar kusan naira miliyan 391.8 duk wata, wanda ya haura naira biliyan 4.7 a shekara.
Gwamnatin jihar ta ce matakin ya biyo bayan sabon tsarin albashin da gwamnatin tarayya ta fara amfani da shi a jami’o’in gwamnatin tarayya, da nufin inganta jin daɗin ma’aikatan jami’o’i da ƙarfafa harkokin ilimi.