Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC, ta rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric, sakamakon matsalar kuɗi da kuma gazawar kamfanin wajen cika wasu muhimman sharuɗɗa.
NERC ta ce matakin ya fara aiki ne daga ranar 10 ga Agustan 2026, bisa tanade-tanaden sashe na 75 zuwa 79 na Dokar Wutar Lantarki ta 2023.
Hukumar ta bayyana cewa Kaduna Electric ya tara bashin sama da naira biliyan 118.6 na wutar lantarki a watan Mayun 2026, wanda ya sa jimillar bashin kamfanin ya kai kusan naira biliyan 456.5.
NERC ta ce a shekarar 2025, kamfanin ya biya kashi 41.93 cikin 100 kacal na kuɗin da aka yi masa ƙiyasin biya.
Haka kuma, hukumar ta ce Kaduna Electric ya samu asarar wutar lantarki da ake samarwa da rarrabawa tare da karɓar kuɗinta da ta kai kashi 71.88 cikin 100.
NERC ta ƙara da cewa kamfanin ya kashe naira biliyan 2.48 kacal wajen inganta ayyukansa, duk da cewa abin da ake buƙata ya kai naira biliyan 24.51.
Hukumar ta kuma bayyana cewa ƙasa da kashi 36 cikin 100 na kwastomomin Kaduna Electric ne ke da mitocin lantarki.
Domin kauce wa tangarda wajen samar da wutar lantarki ga al’ummar yankin, NERC ta ce ta kafa kwamitin wucin gadi na musamman da zai kula da gudanar da kamfanin.
An naɗa Dakta Abdullahi Garba a matsayin shugaban kwamitin, yayin da aka naɗa Dakta Abubakar Umar Hashidu a matsayin mai kula da harkokin kamfanin na tsawon watanni shida.
NERC ta kuma ce Afrexim Bank za ta jagoranci wani shiri na tsawon watanni 12 domin nemo sabbin masu zuba jari da za su maye gurbin babban mai hannun jarin Kaduna Electric.