Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 33 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Rundunar ta ce ta samu sahihan bayanai kan sace fasinjojin ne yayin da suke tafiya a yankin Magazu, inda dakarunta tare da ’yan sandan Tsafe suka fara aikin ceto.
A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar, ya ce jami’an tsaron sun samu labarin lamarin ne da yammacin ranar 8 ga Agusta, 2026.
Ya ce nan take dakarun suka nufi wurin, inda suka yi arangama da ’yan bindigar yayin da suke ƙoƙarin kai waɗanda suka yi garkuwa da su zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Bayan musayar wuta, ’yan bindigar sun tsere cikin daji, inda suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.
Rundunar ta tabbatar da cewa an ceto dukkan fasinjojin 33 cikin koshin lafiya, ba tare da asarar rai ba.
A halin yanzu, dakarun na ci gaba da farautar maharan domin kamo su tare da gurfanar da su a gaban doka.
Kwamandan rundunar ya yaba wa jami’an bisa gaggawar ɗaukar mataki, tare da jaddada aniyar rundunar na ci gaba da kare rayukan jama’a da tabbatar da tsaron manyan hanyoyin sufuri a yankin Arewa maso Yamma.