Batun kisan shahararren mawakin rap, Tupac Shakur, wanda ya kwashe kusan shekaru 30 ba a warware shi ba, yanzu ya shiga matakin shari’a, yayin da mutumin da ake zargi da hannu a kisan nasa zai gurfana a gaban kotu a Las Vegas.
Duane “Keffe D” Davis, mai shekara 63, na fuskantar tuhuma guda ɗaya ta kisan kai da makami mai hatsari, da zargin aikata laifin domin inganta, ci gaba ko taimaka wa wata ƙungiyar masu aikata laifuka, dangane da mutuwar Shakur.
Zaɓen alkalan kotun zai fara ne ranar Litinin, yayin da ake sa ran shari’ar za ta ɗauki kusan wata guda.
Shari’ar za ta sake buɗe ɗaya daga cikin manyan sirrikan duniyar hip-hop, wanda ya shafe shekaru yana ɗaukar hankalin jama’a. Shakur, wanda aka fi sani da 2Pac da Makaveli, ana ɗaukarsa ɗaya daga cikin mawakan rap da suka fi yin tasiri a tarihi.
An harbi Shakur a Las Vegas a ranar 7 ga Satumba, 1996, yayin da yake cikin wata baƙar motar BMW tare da fitaccen mai harkar kiɗa Marion “Suge” Knight, a hanyarsu ta zuwa Club 662, inda Shakur ya shirya yin wasa.
A lokacin da suke tafiya, wata farar motar Cadillac ta zo ta gefensu, inda aka fara harbe-harbe. Shakur, wanda yake zaune a kujerar gaba ta gefen fasinja, an harbe shi sau da dama.
Ya rasu bayan kwanaki shida sakamakon raunukan harbin, yayin da Suge Knight ya tsira.
Binciken kisan ya kwashe shekaru ba tare da samun wani babban ci gaba ba, har zuwa shekarun baya, lokacin da kalaman Davis da ya yi a bainar jama’a, tare da wani littafin da ya rubuta wanda ya ƙunshi bayanai masu yawa, suka sake farfaɗo da binciken.
Davis ya musanta aikata kisan, kuma shari’ar da za a fara yanzu ce za ta kasance muhimmiyar dama ga masu gabatar da ƙara su gabatar da hujjojin da suke da su a gaban kotu.