Uwargidan Gwamnan Jihar Osun, Titilola Adeleke, ta jagoranci zanga-zangar mata a jihar domin nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin kame-kame ba tare da ka’ida ba da kuma tashin hankula, gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar.
Matan, wadanda suka fito daga kungiyoyin ’yan kasuwa da masu sana’o’i daban-daban, sun yi tattaki daga hanyar Osogbo zuwa Ilobu, inda suka nufi hedikwatar rundunar ’yansandan jihar da ke Osogbo.
Adeleke ta bukaci ’yansanda su gudanar da bincike kan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da take zargi da hannu wajen tashin hankulan da ake samu a jihar.
Ta kuma bukaci jami’an tsaro su dakatar da kama-kame da ake zargin ana yi wa magoya bayan jam’iyyun siyasa, tare da tabbatar da cewa zaben zai gudana cikin kwanciyar hankali.
Da yake mayar da martani, Kwamishinan ’Yansandan, Samuel Etaifo, ya ce rundunar na aiki tukuru domin rage tashin hankula a jihar da kuma samar da yanayin da zai bai wa ’yan siyasa damar gudanar da harkokinsu cikin lumana.
Ya gargadi duk wanda zai yi kokarin kawo cikas ga zaben da cewa rundunar ’yan sandan ba za ta lamunci karya doka ba, inda ya ce za a kama duk wanda aka samu da laifin tada hankali ko yin magudin zabe.
Kwamishinan ya kuma yaba wa matan bisa gudanar da zanga-zangar cikin lumana, sannan ya bukace su da su koma gidajensu domin kauce wa duk wani abu da ka iya haifar da sabon tashin hankali.
Ya jaddada cewa ba za a gudanar da zabe cikin inganci ba tare da tsaro ba, don haka jami’an tsaro za su ci gaba da daukar matakan tabbatar da zaman lafiya a jihar kafin da lokacin zaben.