Rundunar ’yan sandan Jihar Kwara ta kama wata mata mai suna Sadiat Yunusa, bisa zargin ta shake ’yar mijinta mai shekaru uku, Ummaiyat har ta mutu a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar.


A cewar ’yan sandan, wadda ake zargin ta bayyana cewa mijinta ya yi watsi da ita da ’ya’yanta uku, tare da fifta kishiyarta da yar ta ta.


’Yan sandan sun ce wadda ake zargin ta yaudari yarinyar ne har ta ja ta zuwa cikin gonaki da ke kusa, inda ake zargin ta kashe ta bayan wata doguwar takaddamar.


Da take ƙarin bayani kan lamarin, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Yuli, bayan mahaifiyar yarinyar ta bar ta a hannun wani ɗan uwata, ta tafi kasuwar ta Kaiama.



Ejire-Adeyemi ta ce jami’an bincike da ke ƙarƙashin Hedikwatar ’Yan Sandan Sashen Kaiama sun fara bincike nan take, wanda ya kai ga cafke wadda ake zargin.


Ta ce wadda ake zargin ta amsa laifin a lokacin da ake yi mata tambayoyi, inda ta shaida wa masu bincike cewa abin da ta aikata ya samo asali ne daga ƙiyayya da kishi sakamakon wata doguwar takaddamar cikin gida.


Ta ce saurin gudanar da bincike ya kai ga cafke wadda ake zargin, wadda a lokacin da ake yi mata tambayoyi ta amsa da kanta cewa ta aikata laifin.