Wani sabon rahoto ya bayyana cewa kuɗin hayar gida mai ɗakuna biyu a wasu manyan unguwannin Lagos Island ya yi matuƙar tashin gwauron zabi, inda ya kai Naira miliyan 17.25

Rahoton Lagos Island Residential Market Report 2026 ya nuna cewa farashin haya ya ƙaru sosai a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2026 a Ikoyi, Victoria Island, Lekki Phase 1 da Ikate.

A Ikoyi, matsakaicin kuɗin hayar gida mai ɗakuna biyu ya kai Naira miliyan 17.25 a shekara, daga Naira miliyan 8 a shekarar 2022.

Victoria Island ce ke biye da Ikoyi, inda hayar gida mai ɗakuna biyu ta kai Naira miliyan 15 a shekara, daga Naira miliyan 6.57 a shekarar 2022.

A Lekki Phase 1 kuma, matsakaicin kuɗin haya ya kai Naira miliyan 10 a shekara, yayin da a Ikate ya kai Naira miliyan 8.5 a shekara, wanda shi ne mafi ƙanƙanta daga cikin yankunan huɗun da rahoton ya bincika.

Rahoton ya danganta tashin farashin hayar da ƙarin buƙatar gidaje, ƙarancin filaye da kuma yawaitar sabbin gidajen alfarma, musamman a wuraren da ’yan kasuwa, manyan ma’aikata, ’yan ƙasashen waje da masu hannu da shuni ke zama