Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci shugabannin addinai da su ci gaba da yin magana a fili kan ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga, da kuma amfani da addini wajen haifar da fitina tsakanin al'umma.


Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Kano, cikin saƙon fatan alheri da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya isar a madadinsa a wajen babban Mauludin Sheikh Ahmad Al-Tijani.


A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Yomi Odunuga, ya fitar, shugaban ya bayyana cewa shugabannin addinai na da muhimmiyar rawa wajen tunkarar tashin hankali, tsattsauran ra’ayi da kuma karkatar da akidar addini domin cimma munanan manufofi.


Ya buƙaci hukumomin addini da ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinsu da su ƙarfafa wayar da kan jama’a game da zaman lafiya, ilimin addini, neman ilimi da kuma tarbiyyar matasa ta fuskar ɗabi’a.


Tinubu ya kuma ce ya kamata shugabannin addinai su yi amfani da tasirinsu wajen inganta adalci, ɗaukar nauyi, tausayi da kuma warware matsalolin da ake samu cikin lumana.