Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara ƙarfafa sa-ido kan tsarin gudanar da shirin rigakafin maganin cizon sauro na Seasonal Malaria Chemoprevention (SMC) na shekarar 2026, bayan kammala wani cikakken bita kan matakan gudanar da shirin, takardun bayanai da kuma tsarin ma’aikatan da za su aiwatar da shi a faɗin jihar.


Wannan na cikin wata Sanarwa mai dauke da sa hannun jami'ar yada labarai ta hukumar Lafiya a matakin farko Sa'adatu Suleiman 


A cewar sanarwar, mataki ya biyo bayan kafa wani kwamitin bincike da Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano ya yi a ranar Laraba, 5 ga Agusta 2026, domin gudanar da bincike kan shirye-shiryen, matakan gudanarwa, rabawa da aiwatar da shirin rabon maganin na shekarar 2026 a jihar. 


Darakta-Janar na Hukumar kula da cututtukan Ƙanjamau ta Jihar Kano (SACA), Dakta Usman Bashir, ne shugaban kwamitin, yayin da Daraktan Gudanarwa na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ke zama sakataren kwamitin.


Bayan tattaunawa da bitar da kwamitin ya gudanar, an yi zama da jami’an Malaria Elimination Programme Officers (MEPOs) daga dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin dubawa tare da daidaita bayanan shirin na kowace ƙaramar hukuma. Haka kuma, an ɗauki wasu matakai domin ƙarfafa gudanarwa, sa-ido da haɗin gwiwar shirin, inda aka naɗa Abdullahi Yusuf Koki a matsayin Mukaddashin Manajan Shirin, Bashir Maikano a matsayin Mukaddashin Jami’in Sa-ido da Bincike na Jiha, sannan Surayya Aminu ta zama Mukaddashiyar Mataimakiyar Jami’in Sa-ido da Bincike ta Jiha.


Haka kuma, an tura wasu jami’an sa-ido da bincike na shiyya guda uku daga Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Jihar Kano domin ƙara ƙarfafa aikin tantance bayanai, daidaita ayyuka da sa-ido a faɗin jihar.


 Bayan kammala aikin tantance bayanai da sauran shirye-shiryen da ake gudanarwa, an tsara fara shirin rigakafin zazzabin cizon sauro na SMC na shekarar 2026 a faɗin Jihar Kano daga ranar Laraba, 12 ga Agusta 2026.


Sai dai kwamitin binciken zai ci gaba da gudanar da aikinsa bisa sharuddan da aka gindaya masa, sannan ya gabatar da cikakken rahoto da shawarwari, ciki har da matakan gyara, na gudanarwa, da kuma hukunci idan ya zama dole ga duk wanda aka samu da laifi.


 Gwamnatin Jihar Kano ta kuma tabbatar wa iyaye, al’ummomi, abokan hulɗar ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki cewa za ta tabbatar da aiwatar da shirin SMC cikin gaskiya, rikon amana, bin ƙa’idoji da ingantaccen tsari, tare da kare sahihancin shirin domin tabbatar da cewa yaran da suka cancanta sun samu cikakkiyar kariya daga zazzabin cizon sauro.