Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce jami’anta sun cafke wani kayan hodar iblis (cocaine) da aka ɓoye cikin cajar wayoyi, wanda ake safararsa zuwa ƙasar Saudiyya.


Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya yi gargadin cewa masu safarar miyagun kwayoyi na ƙara amfani da abubuwan yau da kullum wajen ɓoye miyagun ƙwayoyi domin guje wa kamun jami’an tsaro.


Babafemi ya ce duk da cewa kayan sun yi kama da cajar wayoyi na yau da kullum, jami’an NDLEA ba su yaudare ba, domin bincike ya gano cewa an ɓoye hodar iblis a cikinsu.


Ya ce, “A kallo na farko, waɗannan cajar wayoyi ne, amma jami’an @ndlea_nigeria ba za su faɗa tarkon wannan yaudara ba. Domin an ɓoye kayan hodar iblis a cikinsu, waɗanda ake aikawa zuwa Saudiyya.”


Babafemi ya ce wannan samuwar ta ƙara tabbatar da gargaɗin da hukumar ke yawan yi wa jama’a kan haɗarin amincewa da kai kaya ko jakunkuna a madadin wasu mutane ba tare da gudanar da cikakken bincike ba.


Ya ce, “Shi ya sa muke ci gaba da gargadin mutane kada su taimaka wa wani wajen kai masa kaya ko jaka saboda kawai abin ya bayyana a fili kamar ba shi da matsala, domin masu safarar miyagun ƙwayoyi na amfani da matsananciyar buƙatar mutane wajen yaudararsu.