Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta tsawaita wa’adin miƙa sunayen ’yan takarar kujerar gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi da za su fafata a babban zaɓen ƙasa na Fabrairu 2027.


Wa’adin miƙa sunayen ’yan takarar, wanda bisa sabon jadawalin zaɓe aka tsara zai ƙare ranar Asabar, 8 ga Agusta 2026, yanzu an tsawaita shi zuwa ranar Talata, 11 ga Agusta 2026.


Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon buƙatun da jam’iyyun siyasa suka gabatar na neman ƙarin lokaci domin kammala aikin miƙa sunayen ’yan takararsu.


A wani ci gaba, INEC ta sanar da masu kaɗa ƙuri’a da suka nemi sauya katin zaɓensu na PVC da ya ɓace ko ya lalace, cewa wa’adin buga kwafin katunan da za a iya saukewa daga intanet zai ƙare da tsakar daren Lahadi, 9 ga Agusta 2026.


Hukumar ta ce matakin zai ba ta damar tattara bayanan PVC da aka sauke, domin samar da ƙididdigar ƙarshe ta adadin katunan zaɓe da aka karɓa, gabanin zaɓen gwamnan Jihar Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agusta 2026.


INEC ta kuma jaddada cewa katunan zaɓe da aka sace ba za a iya amfani da su wajen kaɗa ƙuri’a ba.


Hukumar ta tabbatar wa al’ummar Jihar Osun cewa a shirye take ta gudanar da zaɓen gwamna na ranar 15 ga Agusta 2026 cikin ’yanci, adalci, gaskiya da kuma ba tare da nuna wariya ga wani ɓangare ba.