Ƙungiyar SERAP ta buƙaci dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa 19 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta sanar sunayensu, da su bayyana cikakkun bayanan kadarorinsu da basussukan da ake binsi, da na iyalansu sannan kuma, da na ‘ya’yansu da ba su kai shekara 18 ba, gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
SERAP ta kuma buƙaci ‘yan takarar da su bayyana halastattun hanyoyin da suka samo manyan kadarorin da suke da su, tare da barranta mansu da sayen ƙuri’u da kuma bada cin hanci a Lokacin zaɓe.
Ƙungiyar, a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktanta, Kolawole Oluwadare, ya fitar, ta ce ta yi wannan kira ne a cikin wata budaddiyar wasiƙar da ta aikewa ‘yan takarar, mai ɗauke da ranar 8 ga Agusta, 2026.
‘Yan takarar 19 da SERAP ta ambata sun haɗa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu APC da Atiku Abubakar na Jam'iyar ADC sai Peter Obi na NDC da Sanata Sandy Onor na PDP sai muma Omoyele Sowore na AAC da Donald Duke na PRP da Okwori Ada Elizabeth Frederick na NDP da Chukwu Anita Zugwai na YPP da Rufai Adekunle Omoaje na AC da Adenuga Sunday na BT