Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wani tsohon jami’inta, Nwaogu Ihechimere Ezeakolam, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin kasancewa mamba a ƙungiyar IPOB da gwamnatin Najeriya ta haramta.

An gurfanar da Ezeakolam ne ranar Alhamis a gaban Mai Shari’a Mohammed Garba Umar, kan tuhume-tuhume guda huɗu da gwamnatin tarayya ta shigar.

DSS na zargin tsohon jami’in da bai wa IPOB goyon baya da kayan aiki, da kasancewa mamba a ƙungiyar duk da sanin cewa an haramta ta, da kuma wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta domin ƙarfafa mutane su mara wa ƙungiyar baya.

Hukumar ta ce waɗannan ayyuka sun saɓa wa tanade-tanaden Dokar Yaƙi da Ta’addanci ta 2022.

Sai dai bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, Ezeakolam ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.

Mai Shari’a Umar ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa 29 ga Oktoba, sannan ya ba da umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Kuje, har sai an yanke hukunci kan buƙatar belinsa.

A shekarar 2017, gwamnatin Najeriya ta ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci tare da haramta ayyukanta.