Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya kamata jami’o’in ƙasar su fara koyar da ilimin kasuwar hannayen jari (Stock Market) domin bai wa matasa ƙarin ilimi da hanyoyin samar da arziki.

A cewar Tinubu, koyar da wannan fanni a jami’o’i zai taimaka wajen wayar da kan matasa game da yadda kasuwar hannayen jari ke aiki, da kuma yadda za su iya amfani da ita wajen gina jari da samar da makomar tattalin arzikinsu.

Ya ce ƙarin ilimi kan harkokin zuba jari zai taimaka wajen shirya matasa domin su kasance masu fahimtar damar da ke cikin kasuwannin kuɗi da kuma yadda za su iya taka rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.