Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ce ba ta samu wata hujja da ke nuna cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya aikata laifi a cikin badaƙalar wata hukumar gwamnati ta bogi ba.

Hukumar ta bayyana cewa mutumin da ya yi iƙirarin kasancewa Darakta-Janar na Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), Prince Adeniyi Adeyemi, ba gwamnatin tarayya ta naɗa shi ba, kuma takardar naɗin da ya gabatar an gano cewa jabun takarda ce.

ICPC ta kuma ce hukumar da Adeyemi ke ikirarin jagoranta ba a taɓa kafa ta ta hanyar wata doka ko umarnin gwamnati ba.

Shugaban ICPC, Musa Aliyu, ya ce Adeyemi ya kafa wasu hukumomin bogi guda biyu, tare da amfani da takardu na bogi domin ba wa ayyukansa kamannin halattacciyar hukumar gwamnati.

Ya ƙara da cewa Adeyemi ya kutsa cikin ofisoshin tsohuwar Presidential Economic Advisory Council, inda ya yi amfani da wuraren wajen gudanar da ayyukansa.

Hukumar ta ce binciken da ta gudanar bai gano wata shaida da ke nuna cewa gwamnatin tarayya ta amince da hukumar bogin ko kuma ta fitar da kuɗaɗen gwamnati zuwa gare ta ba.