An rantsar da sabon shugaban ƙasar Colombia, Abelardo de la Espriella, inda ya sha alwashin murƙushe abin da ya kira ta’addancin ƙungiyoyin masu fataucin miyagun ƙwayoyi.

An gudanar da bikin rantsar da shi ne a birnin Cali, maimakon babban birnin ƙasar, Bogotá, matakin da ke nuni da mayar da hankali wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke aiki a yankin.

Wakilin BBC ya ruwaito cewa, bayan rantsar da shi, shugaban ya gabatar da jawabi ga dakarun sojin ƙasar a wani sansani, inda ya buƙace su da su tabbatar da doka da ’yancin jama’a a Colombia.

Gwamnatin Donald Trump ta nuna goyon bayanta ga sabon shugaban, tare da yin alkawarin samar masa da tallafin tsaro na biliyoyin daloli domin yaƙi da ƙungiyoyin masu fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran masu ɗauke da makamai.