An naɗa Sheikh Abdulƙadir Jiyali a matsayin Sarkin Takutaha na Ƙasar Hausa, a wani biki da aka gudanar a Fadar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ranar Alhamis 6 ga Agusta 2026.
Bikin naɗin ya samu halartar malamai, shugabanni da ɗimbin masoya Manzon Allah ﷺ, waɗanda suka bayyana farin cikinsu da wannan karramawa.
A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Daura ya ce an yi naɗin ne bisa la’akari da gudummawar Sheikh Abdulƙadir Jiyali wajen cusa son Manzon Allah ﷺ a zukatan al’ummar Musulmi da ƙarfafa bin koyarwarsa.
Ya kuma bayyana fatan cewa wannan sarauta za ta kasance alheri ga al’ummar Hausa.
A nasa jawabin, Sarkin Takutaha na Ƙasar Hausa, Sheikh Abdulƙadir Jiyali, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki, tare da miƙa godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Daura da majalisar masarautar bisa wannan karramawa.
Sheikh Abdulƙadir Jiyali ya roƙi Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa cikin adalci da amana, tare da sanya sarautar ta zama alheri ga Musulunci da al’ummar Hausa.