Wasu ’yan Majalisar Wakilan Najeriya sun buƙaci majalisar tarayya ta dakatar da hutun da take yi, domin gudanar da zaman gaggawa kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa.
’Yan majalisar, waɗanda suka fito daga jam’iyyu daban-daban, sun kafa wata ƙungiya mai suna Save Democracy Group, wadda ta ce manufarta ita ce kare dimokuradiyya da ƙarfafa tsarin mulkin ƙasa.
Ƙungiyar ta buƙaci shugabannin majalisun tarayya guda biyu da su kira zaman gaggawa domin tattauna yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin shekarun 2024, 2025 da 2026, tare da duba wasu batutuwa da suka shafi tafiyar da harkokin ƙasa.
Sun ce akwai buƙatar majalisar ta ci gaba da gudanar da aikinta a wannan lokaci, maimakon ci gaba da hutun da take yi, saboda muhimmancin batutuwan da ke gabanta.