Ƙungiyar Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya (NGX Group) ta bayyana cewa darajar kasuwar kamfanonin da aka jera a kasuwar hannayen jari ta ƙaru daga kusan Naira tiriliyan 30 a watan Mayun 2023 zuwa sama da Naira tiriliyan 150 a halin yanzu.
Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NGX Group, Temi Popoola, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da shi da shugaban NGX da Darakta Janar na Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari (SEC) suka yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Popoola ya ce tawagar ta yi wa Shugaban Ƙasa bayani kan yadda kasuwar hannayen jari ke bunƙasa, damar da ke akwai na ci gaba da faɗaɗa ta, da kuma matakan da ake buƙata domin jawo ƙarin masu zuba jari.
Ya bayyana cewa idan aka ci gaba da wannan ci gaba, ana sa ran darajar kasuwar za ta kai kusan Naira tiriliyan 230 kafin ƙarshen shekarar 2026, musamman idan aka jera manyan kamfanoni a kasuwar.
A cewarsa, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake sa ran za su ƙara darajar kasuwar shi ne shirin jera Matatar Dangote (Dangote Refinery) a kasuwar hannayen jari.
“A watan Mayun 2023 lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki, darajar kasuwar ba ta kai Naira tiriliyan 30 ba. Yanzu ta haura Naira tiriliyan 150,” in ji Popoola.
Ya ce wannan ci gaban ya samar da ɗimbin arziki ga masu zuba jari da kamfanoni, inda ya kiyasta cewa tsakanin mutane 500,000 zuwa 900,000 sun zama masu kuɗin miliyoyi sakamakon ribar da suka samu daga kasuwar hannayen jari.
Popoola ya kuma bayyana cewa ribar kamfanoni da dama da ke kasuwa ta ƙaru matuƙa, inda wasu suka ninka ribarsu har sau biyar tun daga shekarar 2023.
Ya danganta wannan bunƙasa da sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, ciki har da cire tallafin man fetur, gyaran tsarin canjin kuɗaɗen waje, da kuma sabuwar Dokar Zuba Jari da Kasuwancin Hannayen Jari da aka sanya wa hannu a shekarar 2025.
Haka kuma ya ambaci shirin ƙara jarin bankuna da sauye-sauyen fasahar zamani a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen bunƙasa kasuwar.
A cewarsa, bankunan Najeriya sun tara sama da Naira tiriliyan 4 ta hanyar ƙarin jari, kuma ana sa ran adadin zai haura Naira tiriliyan 5 kafin ƙarshen wannan shekara, galibi daga masu zuba jari na cikin gida.
Popoola ya ce NGX ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hanzarta aiwatar da shirin sayar da hannun jarin gwamnati a wasu manyan kamfanoni tare da jera su a kasuwar hannayen jari.
Daga cikin kamfanonin da aka ba da shawarar a jera akwai Nigeria LNG (NLNG), Indorama, da kuma wasu kadarorin Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Limited).
Ya kuma ce sun roƙi gwamnatin ta samar da ƙarin tallafi da ƙarfafawa domin kamfanoni masu zaman kansu su riƙa jera hannayen jarinsu a kasuwar Najeriya maimakon zuwa ƙasashen waje.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa tawagar da cikakken goyon bayansa wajen ci gaba da aiwatar da manufofin da za su bunƙasa kasuwar hannayen jari.
Shi ma Shugaban NGX Group, Alhaji Umaru Kwairanga, ya bayyana cewa kasuwar hannayen jarin Najeriya na daga cikin kasuwannin da suka fi bunƙasa a duniya a baya-bayan nan.
Ya danganta wannan nasara da sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, waɗanda suka ƙara wa masu zuba jari ƙarfin gwiwa.
A nasa ɓangaren, Darakta Janar na Hukumar SEC, Dakta Emomotimi Agama, ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau domin tabbatar da daidaito, gaskiya da ci gaban kasuwar hannayen jari ta Najeriya.