Gwamnatin Birtaniya ta sanar da naɗin Ms Vicky Seymour a matsayin sabuwar Mataimakiyar Babbar Jakadiyar Birtaniya a Abuja.
A cikin wata sanarwa da Babbar Hukumar Jakadancin Birtaniya ta fitar, an bayyana cewa Seymour ta maye gurbin Mrs Gill Lever OBE, wadda ta kammala aikinta a Najeriya a watan Yunin 2026.
Sanarwar ta ce Vicky Seymour ta riga ta fara aiki a Abuja, inda za ta taimaka wajen ƙarfafa dangantakar Birtaniya da Najeriya a fannoni daban-daban.
Waɗannan fannoni sun haɗa da bunƙasa tattalin arziki, tsaro, harkokin ƙaura da shige da fice, ci gaban al'umma, haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, da kuma ƙarfafa alaƙar jama'ar ƙasashen biyu.
Jakadancin Birtaniya ya bayyana cewa naɗin Seymour wani ɓangare ne na ƙoƙarin ci gaba da faɗaɗa haɗin gwiwa da Najeriya a muhimman fannoni masu amfani ga ƙasashen biyu.