Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda (Police Service Commission – PSC) ta miƙa sabbin jami’an ’yan sanda 50,000 da aka ɗauka aiki ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya domin fara horo, a wani mataki na ƙara ƙarfafa ƙarfin aikin tsaro a faɗin ƙasar.

A cikin wata sanarwa da Hukumar ta fitar, ta ce ɗaukar sabbin jami’an ya gudana ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da bin dukkan tanade-tanaden doka da suka shafi aikin.

Hukumar ta bayyana cewa an miƙa jerin sunayen waɗanda suka yi nasara a aikin ɗaukar ma’aikatan ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya domin a tura su zuwa cibiyoyin horo da aka tanada.

Da yake wakiltar Sufeto Janar na Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, DIG Isyaku Mohammed ya yaba da yadda aka gudanar da aikin ɗaukar sabbin jami’an cikin gaskiya da adalci.

Ya kuma tabbatar da cewa za a fara horas da sabbin jami’an a cibiyoyin horo da ke faɗin ƙasar da zarar gwamnatin tarayya ta saki kuɗaɗen da ake buƙata domin gudanar da horon.

Haka kuma, Ma’aikatar Harkokin ’Yan Sanda da Sakataren Hukumar PSC sun yabawa sahihancin aikin ɗaukar ma’aikatan, suna mai bayyana cewa an samu nasarar gudanar da shi ne sakamakon kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki.

Hukumar ta ce wannan mataki wani muhimmin ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na ƙara yawan jami’an tsaro da inganta aikin rundunar domin samar da ingantaccen tsaro ga al’ummar Najeriya.