Sufeto Janar na Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya amince da tura sabbin Kwamishinonin ’Yan Sanda (CPs) zuwa wasu jihohi da manyan sassan rundunar a faɗin ƙasar, bayan Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda (Police Service Commission) ta amince da shawarwarinsa.
A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, CSP Ani Iniedu, ya fitar, matakin na da nufin ƙarfafa ingancin ayyukan tsaro, bunƙasa shugabanci a rundunar, da kuma ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da ake yi domin inganta aikin ’yan sanda.
Sabbin Kwamishinonin da aka tura zuwa jihohi sun haɗa da:
- Jihar Abia – CP Afolabi Wilfred Olutokunbo
- Jihar Plateau – CP Ayodeji Faniyan
- Jihar Bayelsa – CP Saka Adewale Ajao
- Jihar Cross River – CP Ajo Geofrey Ordue
- Jihar Anambra – CP Nanna Oji Ama
- Jihar Edo – CP Patrick Daaor
- Jihar Jigawa – CP Tani Murtala
- Jihar Delta – CP Samuel Erale
Haka kuma, an tura wasu manyan jami'ai zuwa muhimman sassa na rundunar, ciki har da Sashen Bayanai na Sirri (FID), Sashen Binciken Manyan Laifuka (FCID), Sashen Yaki da Safarar Bil Adama, Sashen Yaki da Ta'addanci (CTU), Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda, Kwalejin Horar da ’Yan Sanda ta Jos, Kwalejin ’Yan Sanda ta Kano (POLAC), da sauran muhimman cibiyoyi a Abuja, Lagos, Kaduna da Gombe.
IGP Olatunji Rilwan Disu ya umarci jami’an da aka tura sabbin mukamai da su yi amfani da ƙwarewarsu wajen ƙarfafa aikin binciken sirri, inganta ayyukan tsaro, tabbatar da ƙwarewa da gaskiya a aikin ’yan sanda, tare da zurfafa alaƙa tsakanin rundunar da al’umma domin inganta tsaro a faɗin Najeriya.