Kafofin yaɗa labarai na Isra'ila sun ruwaito cewa shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Mossad, Roman Goffman, ya sallami wasu manyan jami'ai biyu na hukumar bisa zargin cewa su ne suka tsara wani shirin sirri da bai yi nasarar kifar da gwamnatin Iran ba.
A cewar tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra'ila, ɗaya daga cikin jami'an da aka kora ya jagoranci sashen tattara bayanan sirri na Mossad tun watan Disamban 2015, yayin da ɗayan kuma ke shugabantar sashen da ke kula da harkokin Iran. Sai dai ba a bayyana sunayensu ba.
Rahoton ya ce jami'an biyu sun tsara wani shirin sirri da nufin kifar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar amfani da wasu ƙungiyoyin Kurdawa tare da tayar da zanga-zangar gama-gari a sassa daban-daban na ƙasar.
Har ila yau, rahotannin sun bayyana cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya gabatar da wannan shiri ga Shugaban Amurka, Donald Trump, a lokacin da yake ƙoƙarin shawo kansa ya amince da kai hari kan Iran a watan Maris.
Rahoton ya ƙara da cewa lokacin da aka tsara shirin, David Barnea ne ke jagorantar Hukumar Mossad, kafin daga bisani Roman Goffman ya maye gurbinsa a watan Yunin wannan shekara.
Sai dai har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Isra'ila ko Hukumar Mossad da ta tabbatar ko ta musanta wannan rahoto.