Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wani tsohon jami'inta, Nwaogu Ihechimere Ezeakolam, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin kasancewa mamba a haramtacciyar ƙungiyar IPOB (Indigenous People of Biafra).

An gurfanar da shi ne a ranar Alhamis a gaban Mai Shari'a Mohammed Garba Umar kan tuhume-tuhume guda huɗu da Gwamnatin Tarayya ta shigar a kansa.

DSS na zargin Ezeakolam da bai wa IPOB goyon baya ta hanyar samar mata da kayan aiki, shiga ƙungiyar duk da sanin cewa an haramta ayyukanta, da kuma wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta domin ƙarfafa jama'a su mara mata baya.

Hukumar ta ce waɗannan ayyuka sun saɓa wa tanade-tanaden Dokar Yaƙi da Ta'addanci ta 2022.

Sai dai bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, Ezeakolam ya musanta aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.

Mai Shari'a Mohammed Garba Umar ya ɗage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa 29 ga Oktoba, domin fara sauraron ƙarar, sannan ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a Gidan Gyaran Hali na Kuje har sai an yanke hukunci kan buƙatar belinsa.

A shekarar 2017, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta'addanci tare da haramta dukkan ayyukanta a faɗin ƙasar.