Wata kotu a Amurka ta ci kamfanin Meta, mai mallakar shafukan Facebook da Instagram, tarar dala miliyan 567 saboda gazawarsa wajen kare lafiyar yara da matasa masu amfani da shafukan sada zumunta.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan ita ce mafi girman tara da aka taɓa kakaba wa kamfanin Meta a irin wannan shari'a.
Alƙalin da ya yanke hukuncin ya ce Meta ya taka rawa wajen ƙara matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa da damuwar da wasu yara da matasa ke fuskanta sakamakon yadda suke amfani da shafukan Facebook da Instagram.
Kotun ta kuma umarci kamfanin da ya yi sauye-sauye a tsarin amfani da shafukansa ga yara da matasa, bayan gano cewa wasu fasalolin dandalin na iya yin illa ga lafiyar ƙwaƙwalwarsu.
Sai dai Meta ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa ta riga ta samar da tsauraran ƙa'idoji da matakan kariya domin tabbatar da tsaron yara a shafukanta.
Kamfanin ya kuma sanar da cewa zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun, yana mai bayyana cewa bai amince da hukuncin da aka yanke masa ba.