Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da Ƙungiyar Ma’aikata ta TUC sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan ma’aikatan Najeriya mafi ƙarancin albashi na Naira 500,000.

Mataimakin Shugaban Ƙasa na NLC kuma Shugaban Ƙungiyar Malaman Najeriya (NUT), Kwamared Audu Titus Amba, ne ya bayyana wannan buƙata yayin taron Nigeria Rights of Workers Summit da aka gudanar a ranar Alhamis a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.

Kwamared Amba, wanda ya wakilci Shugaban NLC na ƙasa, Kwamared Joe Ajaero, ya ce wa’adin yarjejeniyar albashin mafi ƙaranci na N70,000 da aka cimma tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya ya ƙare tun a watan Yuli.

Ya ce saboda haka ƙungiyoyin za su sake shiga tattaunawa da Gwamnatin Tarayya domin neman a amince da N500,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ƙasar.

A cewarsa, la’akari da halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ma’aikata ke fuskanta, duk wani albashi da bai kai N500,000 ba ba zai wadatar da buƙatunsu ba.

Sai dai ya jaddada cewa NLC ba ta neman yin fito-na-fito da Gwamnatin Tarayya ba, illa dai tana son a sake duba tsarin albashi domin inganta rayuwar ma’aikata.

Kwamared Amba ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, bisa samar da yanayi mai kyau da ya ba da damar gudanar da taron, wanda ya samu halartar kusan wakilai 1,000 daga sassan ƙasar.

Ya ce mahalarta taron sun tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi walwalar ma’aikata da shugabancin ƙungiyoyin ƙwadago, tare da fito da shawarwarin da za su taimaka wajen inganta harkokin ma’aikata.

Shi ma wakilin Shugaban Ƙasa na TUC, Kwamared Nuhu Toro, ya ce ma’aikatan Najeriya na buƙatar a ɗauki matakai na zahiri maimakon alkawura, yana mai jaddada cewa albashin da zai iya biyan buƙatun rayuwa shi ne mafita ga inganta rayuwar ma’aikata.

Haka kuma ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su kawo ƙarshen ɗaukar ma’aikata na wucin gadi (casualisation of labour), yana mai cewa tabbataccen aikin yi zai ƙara ƙwazon ma’aikata tare da bunƙasa tattalin arziki.

Da yake ƙaddamar da taron, Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya tunatar da mahalarta cewa shi ne gwamna na farko a Najeriya da ya fara aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N75,000 ga ma’aikatan jiharsa.

Ya kuma yi alƙawarin gabatar da sabon buƙatar ƙungiyoyin ƙwadago ta albashin N500,000 a ɗaya daga cikin tarukan Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya domin a tattauna ta.