Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta bayyana cewa sabon tsarin da ta bullo da shi na mayar da aikin buga fasfo zuwa Abuja bai shafi rajista ko karɓar fasfo a ofisoshinta na jihohi ba.

Hukumar ta ce rahotannin da ke yawo cewa an cire cibiyoyin gudanar da fasfo daga Kano ba gaskiya ba ne, tana mai cewa an samu kuskuren fahimtar manufar sabon tsarin.

Wannan bayani ya biyo bayan cece-ku-ce da ya biyo bayan yaɗuwar wata takarda da ke nuna cewa an mayar da wasu cibiyoyin buga fasfo daga jihohi zuwa Abuja.

Da yake zantawa da BBC, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Shige da Fice a Jihar Kano, DSI Muhammad Auwal, ya ce an fara aiwatar da sabon tsarin tun farkon shekarar nan, kuma ana aiwatar da shi a jihohi a matakai daban-daban.

"Ba wai za a daina yin rajistar fasfo ko karɓarsa a jihohi ba ne. Abin da aka mayar zuwa Abuja shi ne aikin buga fasfo kawai," in ji shi.

Ya bayyana cewa an fara aiwatar da tsarin a jihohin Nasarawa, Kogi, Borno da Yobe, kuma za a ci gaba da faɗaɗa shi zuwa sauran jihohin ƙasar.

DSI Muhammad Auwal ya kuma tabbatar da cewa takardar da ake yaɗawa ta fito ne daga hukumar, amma ya ce takarda ce ta cikin gida wadda ba a yi niyyar fitar da ita bainar jama'a ba.

A cewarsa, manufar mayar da aikin buga fasfo zuwa wuri guda ita ce ƙarfafa tsaro, inganta tsarin gudanarwa da kuma rage yiwuwar buga fasfo na bogi.

Dangane da rashin ganin Jihar Legas cikin jerin jihohin da aka ambata, jami’in ya ce Legas ma tana cikin rukuni na biyar na aiwatar da shirin, kuma za a fara amfani da sabon tsarin a can nan ba da jimawa ba.