Shirin na gudana ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Kaduna Markets Development and Management Company (KMDMC) da Kaduna Geographic Information Service (KADGIS), domin bai wa masu shaguna da sauran kadarorin kasuwanci da suka cancanta damar samun Takardar Shaidar Mallaka (Certificate of Occupancy – C of O) ga kowane shago ko rukunin kasuwanci da suka mallaka.
Sabon tsarin ya shafi shaguna da ke cikin kasuwanni, manyan cibiyoyin kasuwanci (shopping malls), plazas da sauran gine-ginen kasuwanci masu ɗauke da raka’o’i da dama.
Ana sa ran tsarin zai tabbatar da ingantacciyar mallaka ta doka, kare haƙƙin masu kadarori, ƙara darajar kadarorin kasuwanci, tare da sauƙaƙa wa masu kadarori samun rance daga cibiyoyin kuɗi ta hanyar amfani da kadarorinsu a matsayin jingina.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin, Manajan Daraktan KMDMC, Alhaji Ahmed Shehu Haruna, ya bayyana wannan tsari a matsayin wani babban ci gaba wajen zamanantar da tsarin gudanar da kadarorin kasuwanci a Jihar Kaduna.
Ya yabawa Darakta Janar na KADGIS, Dakta Bashir Garba Ibrahim, bisa jagoranci da ƙoƙarin da ya yi wajen ganin an aiwatar da shirin, yana mai cewa hakan ya samo asali ne daga shekaru na aiki domin inganta tsarin kula da filaye da kuma buɗe sabbin damammaki ga masu kadarori.
Har ila yau, ya miƙa godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa hangen nesa, goyon bayan siyasa da kuma ƙudurin tabbatar da aiwatar da wannan muhimmin sauyi.
A cewarsa, duk da cewa an taɓa yunƙurin aiwatar da tsarin Sectional Titling a baya, bai samu nasara ba, sai dai gwamnatin Sanata Uba Sani ta nuna ƙudurin ganin an aiwatar da shi cikin nasara.
A yayin bikin ƙaddamar da shirin, an kuma miƙa Takardun Shaidar Mallaka (Certificates of Occupancy) na farko ga waɗanda suka fara cin gajiyar shirin, lamarin da ya nuna buɗe sabon babi a fannin mallakar kadarorin kasuwanci a Jihar Kaduna.
Kamfanin KMDMC ya bayyana cewa wannan tsari zai ƙara ƙarfin gwiwar masu zuba jari ta hanyar tabbatar da ingantacciyar mallaka, sauƙaƙa samun rance, ƙarfafa zuba jari daga masu zaman kansu, da kuma haɓaka darajar tattalin arzikin kadarorin kasuwanci.
Saboda haka, kamfanin ya buƙaci duk masu shaguna da sauran kadarorin kasuwanci da suka cancanta a kasuwanni, cibiyoyin kasuwanci, plazas da makamantansu da su yi amfani da wannan dama ta hanyar fara aiwatar da matakan samun Takardar Shaidar Mallaka bisa ƙa’idojin da aka tanada.
KMDMC ta kuma sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da KADGIS da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar wannan shiri, tare da ƙara bunƙasa zuba jari, inganta kasuwanni da kuma ƙarfafa tattalin arzikin Jihar Kaduna.