Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da mayar da ma’aikata 37 na Hadaddiyar Hukumar Ma’aikatan Kananan Hukumomi (Unified Local Government Service) da aka kora ba bisa ka’ida ba a lokacin gwamnatin tsohon gwamna, Malam Nasir El-Rufai.

Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Jihar Kaduna, Farfesa Aminu Suleiman, ne ya bayyana hakan yayin da yake miƙa takardun komawa bakin aiki ga ma’aikatan da abin ya shafa a Kaduna.

A cewarsa, matakin ya biyo bayan rahoton wani kwamitin bincike da gwamnatin da ta gabata ta kafa bayan ma’aikatan sun shigar da ƙorafi kan korarsu daga aiki. Kwamitin ya tabbatar da cewa an kore su ba tare da bin ƙa’idojin aiki ba, tare da ba da shawarar a mayar da su bakin aiki, sai dai ba a aiwatar da shawarar ba.

Ya ce bayan ma’aikatan sun sake gabatar da ƙorafinsu ga gwamnatin Sanata Uba Sani, Hukumar ta sake nazarin lamarin tare da miƙa shawarwari ta hanyoyin gwamnati da suka dace. Bayan tabbatar da cewa an zalunce su, gwamnan ya amince da mayar da su bakin aiki nan take.

Farfesa Aminu Suleiman ya bayyana cewa daga cikin ma’aikatan 37, wasu sun rasu yayin da wasu suka yi ritaya kafin a amince da mayar da su aiki. Ya ce waɗanda har yanzu suke cikin shekarun aiki za su koma bakin aikinsu nan take, yayin da za a biya waɗanda suka yi ritaya dukkan haƙƙoƙinsu. Haka kuma, iyalan waɗanda suka rasu za su karɓi kuɗaɗen da suka dace da su.

Ya yabawa Gwamna Uba Sani bisa nuna jajircewa wajen tabbatar da adalci da kare haƙƙin ma’aikata, yana mai cewa wannan mataki ya nuna gwamnatin na sauraron koke-koken al’umma tare da warware su cikin gaskiya da adalci.

Har ila yau, ya gode wa Shugaban Ma’aikatan Jihar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Ma’aikatar Kananan Hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki saboda gudunmawar da suka bayar wajen ganin an aiwatar da wannan mataki.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kaduna, Ayuba Suleiman, ya bayyana matakin a matsayin wata shaida ta yadda gwamnatin Uba Sani ke mutunta ma’aikata da tabbatar da adalci.

Ya kuma nuna damuwa cewa adadin ma’aikatan Hadaddiyar Hukumar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ya ragu daga sama da mutum 16,000 a shekarar 2014 zuwa fiye da mutum 3,000 kaɗai a halin yanzu, tare da bayyana cewa ana sa ran kusan ma’aikata 800 za su yi ritaya kafin ƙarshen shekarar nan.

Shi ma Shugaban Ƙungiyar TUC reshen Kaduna, Abdullahi Dan Fulani, ya yaba da matakin, tare da roƙon gwamnati da ta tabbatar an biya dukkan haƙƙoƙin ma’aikatan cikin gaggawa.

Da take jawabi a madadin ma’aikatan da aka mayar bakin aiki, Michal Anga ta gode wa Gwamna Uba Sani bisa dawo da su bakin aiki bayan shekaru na neman adalci.

Ta ce duk da cewa an shawarce su su garzaya kotu, sun zaɓi bin hanyoyin da doka ta tanada, kuma haƙurinsu ya haifar da nasara. Ta bayyana matakin a matsayin gagarumar nasara ga adalci da juriya.

A ƙarshe, ma’aikatan sun gode wa Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi da sauran jami’an gwamnati da suka taka rawa wajen tabbatar da dawo da su bakin aiki.