An bai wa ’yan jarida a Jihar Kano horo kan dabarun nazarin bayanan kiwon lafiya da kuma bibiyar ayyukan cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko (PHC), a wani yunƙuri na ƙarfafa ɗaukar alhaki da inganta ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.


Taron horaswar na kwanaki biyu, wanda Ƙungiyar International Society of Media in Public Health (ISMPH), tare da EngenderHealth Consortium Partnership da Unified Health Media Network, suka shirya, ya samu halartar ’yan jarida daga gidajen Jaridu daban - daban


Da yake jawabi a wajen taron, Daraktan gudanarwa na ISMPH, dakta Moji Makanjuola, wanda Manajan Shirye-shiryen ƙungiyar, Philip Muoneke, ya wakilta, ya ce ’yan jarida na da muhimmiyar rawar da zasu taka wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana a fannin kiwon lafiya a Najeriya, ta hanyar gabatar da rahotanni bisa sahihan bayanai da hujjoji.


Ya bayyana cewa tabbatar da gaskiya a fannin kiwon lafiya bai tsaya ga hukumomin gwamnati kaɗai ba, akwai buƙatar kafafen yaɗa labarai subrika bibiya tare yin tambayoyi masu muhimmanci, don tabbatar da sahihancin bayanai da kuma amfani da ingantattun bayanai domin sanya hukumomin gwamnati gudanar da aiki yadda ya kamata don inganta harkokin kiwon Lafiya


A cewarsa, ingantaccen shugabanci a fannin kiwon lafiya bai dogara kawai da samun sahihan bayanai ba, akwai buƙatar ’yan jarida masu ƙwarewar fahimtar bayanan fasaha da sauya su zuwa rahotanni masu sauƙin fahimta, waɗanda za su taimaka mutane wajen neman ingantattun ayyukan kiwon lafiya.


A yayin taron, an koyar da ’yan jaridar yadda za su fahimci da kuma amfani da Primary Health Care Accountability Scorecards, sakamakon Integrated Supportive Supervision (ISS), da Primary Health Care Facility Assessment Tool (PHC-FAT), da kuma hanyoyin bibiyar yadda ake samar da kuɗaɗen kiwon lafiya da kuma yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin fannin.