Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya karɓi baƙuncin tawagar shugabannin Gidauniyar Gates (Gates Foundation) a wani liyafar cin abinci da aka shirya a Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ofishin Afirka da Indiya kuma Babban Jami'in Tsare-tsare na gidauniyar, Ankur Vora.

A cewar gwamnan, ziyarar tawagar na nuna irin ƙaƙƙarfan haɗin gwiwar da ke tsakanin gwamnatin jihar da gidauniyar, tare da ba da damar duba irin ci gaban da aka samu wajen ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na matakin farko, bunƙasa binciken kimiyya da ake jagoranta a cikin gida, da kuma gina ingantattun tsarin tattara bayanai domin tallafa wa yanke shawara bisa hujjoji.

Uba Sani ya bayyana cewa tattaunawar ta bai wa ɓangarorin biyu damar nazarin ayyukan da ake gudanarwa, musayar ra'ayoyi da kuma ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa domin samar da sakamako mai ɗorewa ga al'ummar Jihar Kaduna.

Ya ce ya ji daɗin kalaman Ankur Vora, wanda ya bayyana cewa a tattaunawar da ake yi a hedikwatar Gidauniyar Gates ta duniya, Kaduna na ci gaba da kasancewa jiha mafi muhimmanci da gidauniyar ke haɗin gwiwa da ita a Najeriya. A cewarsa, wannan yabo na nuna irin ƙudirin gwamnatin jihar wajen saka hannun jari a fannonin kiwon lafiya, ilimi, noma da bunƙasa jarin ɗan Adam.

Gwamnan ya kuma gode wa Gidauniyar Gates bisa zaɓar Kaduna a matsayin jiha ta farko da tawagar shugabanninta ta ziyarta a Najeriya, yana mai cewa hakan alama ce ta amincewa da manufofin sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa da kuma haɗin gwiwar da ta gina da ƙungiyoyin ci gaba.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa wannan haɗin gwiwa domin inganta rayuwar al'umma, faɗaɗa damar ci gaba da kuma haɓaka ci gaba mai ɗorewa da ya haɗa kowa a faɗin Jihar Kaduna.