Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta ci gaba da nuna ƙuduri wajen inganta harkokin lafiya, musamman ta fuskar kula da mata masu juna biyu da ƙananan yara a faɗin jihar.
Tun bayan hawan wannan gwamnati kan mulki, Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano, bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta samar da kayayyakin kula da mata masu juna biyu, waɗanda ake rabawa a ƙarshen kowane wata zuwa manyan asibitocin gwamnati da ke sassa daban-daban na jihar.
An samar da waɗannan kayayyaki ne domin ƙarfafa ayyukan kula da mata masu juna biyu, musamman waɗanda ke buƙatar kulawa ta musamman ko kuma waɗanda za a yi wa tiyatar haihuwa (Cesarean Section), tare da rage haɗarin da ka iya tasowa yayin haihuwa.
Gwamnatin jihar ta jaddada cewa wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na inganta kiwon lafiyar uwa da jariri, tare da tabbatar da cewa al'ummar Kano suna samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya a cibiyoyin gwamnati.