Rundunar Operation HADIN KAI ta sanar da samun wani gagarumin ci gaba a yaƙin da take yi da ƙungiyar ISWAP/ISIS, bayan jerin hare-haren da ta kai kan sansanonin ƴan ta'addan a yankin Tafkin Chadi da ke Arewacin Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Jami'in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ya ce dakarun sun ƙwato wasu muhimman na'urorin sadarwa da bayanan sirri, ciki har da kyamarar bidiyo (camcorder) da ƴan ISWAP ke amfani da ita wajen ɗaukar bidiyoyin farfaganda da kuma rubuce-rubucen ayyukansu.

Sanarwar ta ce binciken ƙwararru da aka gudanar kan waɗannan na'urori ya samar da muhimman bayanan sirri da suka taimaka wajen gano wuraren da ƴan ta'addan ke aiki da kuma tantance wasu manyan jagororinsu da ke gudanar da ayyuka a yankin Mangari–Metele–Dogon Chukun, da ke ƙananan hukumomin Abadam da Kukawa na Jihar Borno.

Daga cikin waɗanda rundunar ta gano akwai Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa, wanda ake yi wa laƙabi da Wali, kuma ake zargin shi ne gwamnan ISWAP a yankin Yammacin Afirka. Haka kuma akwai mataimakinsa Muhammad Jidda, wanda aka fi sani da "Mai Hannu Ɗaya", da kuma Hamad Abu Hanifa, wanda ake zargin shi ne Amirul-Fiya na ƙungiyar.

Operation HADIN KAI ta bayyana cewa Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa shi ne babban jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a yankin Tafkin Chadi a halin yanzu.

Rundunar ta ce za ta bayar da tukwici mai tsoka ga duk wanda ya bayar da sahihan bayanan da za su kai ga cafke shi, tare da tabbatar da cewa za a kiyaye sirrin duk wanda ya bayar da bayanai da kuma kare asalinsa bisa ƙa'idojin tsaro.

Ta kuma yi kira ga al'umma da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani sahihin bayani da zai taimaka wajen gano ko cafke waɗanda ake zargi ta hanyoyin da aka tanada ko kuma ta lambar waya 0708 498 8859.

Sai dai rundunar ta gargaɗi jama'a da kada su yi ƙoƙarin tunkarar ko kama waɗanda ake nema da kansu, tare da jaddada cewa ya kamata a bar irin waɗannan ayyuka ga jami'an tsaro.