Ƙungiyar Makinde Reset Nigeria Volunteers and Reset Agents ta sanar da fara rajistar masu sa kai a faɗin ƙasar domin tallafa wa burin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin haɗakar jam'iyyun APM/PDP.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a Abuja, ta ce an buɗe rajistar ne tun daga ranar Litinin, kuma ta samu karɓuwa daga masu sha'awa a jihohi 36 na Najeriya, Babban Birnin Tarayya (FCT) da kuma 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.

Ƙungiyar ta bayyana cewa shirin na da nufin gina wata babbar cibiyar masu sa kai a faɗin ƙasar domin yaɗa Ajandar Reset Nigeria, wadda ta ce wata manufa ce da ke mayar da hankali kan sake farfaɗo da Najeriya ta hanyar gyaran cibiyoyin gwamnati da bunƙasa tattalin arziki.

Sanarwar ta ce ajandar ta kuma haɗa da inganta tsaro, samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya, ilimi, wutar lantarki, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa ababen more rayuwa masu ɗorewa.

Masu shirya shirin sun bayyana cewa rajistar za ta taimaka wajen haɗa masu goyon baya da masu sa kai daga sassa daban-daban na ƙasar domin shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.