Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ma'aikatan gwamnati cewa za ta fara biyan ragowar kuɗin tallafin albashi (Wage Award) kafin 15 ga watan Agusta, yayin da kuma ake ci gaba da shirye-shiryen biyan bashin karin girma (Promotion Arrears) ga ma'aikatan da abin ya shafa.
Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ne ya ba da wannan tabbaci yayin wata ganawa da shugabannin Joint Public Service Negotiating Council (JPSNC).
A cewarsa, gwamnati na kammala shirye-shiryen fitar da kuɗaɗen da ake buƙata domin biyan tallafin albashin, kuma ma'aikatan da suka cancanta za su fara karɓar kuɗinsu kafin tsakiyar watan Agusta.
Ministan ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da aiwatar da biyan bashin karin girma, ciki har da Batch 7, wanda a baya bai samu shiga cikin tsarin biyan ba, tare da Batch 9.
Ya ƙara da cewa gwamnati na kuma aiki kan batun peculiar allowance da sauran kuɗaɗen da ake bin ma'aikata.
Taiwo Oyedele ya jaddada cewa gwamnatin tarayya na da niyyar cika duk alkawuran da ta ɗauka wa ma'aikata ta hanyar ci gaba da tattaunawa da kuma ɗaukar matakan da suka dace cikin gaggawa, domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito a harkokin ma'aikatan gwamnati.
A nasa ɓangaren, shugabannin ƙungiyoyin ma'aikata sun yi maraba da wannan tabbaci, tare da yin kira ga gwamnati da ta gaggauta aiwatar da duk sauran yarjejeniyoyin da har yanzu ba a cika ba.