Hukumar Nigerian Independent System Operator (NISO) da Babbar Hukumar Jakadancin Kanada a Najeriya sun tattauna kan hanyoyin haɗin gwiwa da za su taimaka wajen bunƙasa fannin wutar lantarki a Najeriya ta hanyar haɓaka ƙwarewa, musayar fasaha, haɗa makamashi mai sabuntawa da kuma zuba jari a muhimman ayyukan samar da wutar lantarki.

Tattaunawar ta gudana ne a hedikwatar NISO da ke Abuja, lokacin da Babban Kwamishinan Kanada a Najeriya, David Sproule, ya jagoranci wata tawaga domin kai ziyara ga hukumar.

Daraktan Janar na NISO, Abdu Mohammed, ya shaida wa tawagar Kanada cewa hukumar na jagorantar shirin zamanantar da masana'antar wutar lantarki ta Najeriya ta hanyar sauya tsarin zuwa na zamani.

Ya ce daga cikin manyan ayyukan da NISO ke aiwatarwa akwai kafa Tsarin SCADA (Supervisory Control and Data Acquisition) da Energy Management System (EMS), gina sabbin dandamalin cinikin kasuwar wutar lantarki, da kuma amfani da tsarin Telemetry da Advanced Metering Infrastructure (AMI) domin inganta gudanar da kasuwar wutar lantarki.

Abdu Mohammed ya kuma bayyana cewa NISO na taka muhimmiyar rawa wajen tsara da kuma tantance ayyukan faɗaɗa layukan wutar lantarki na ƙasa, gano wuraren da suka fi buƙatar saka hannun jari, haɗa makamashi mai sabuntawa cikin tsarin wutar lantarki na ƙasa, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu ta hanyar tsarin Public-Private Partnership (PPP).

Ya bayyana cewa bunƙasa ƙwarewar ma'aikata, shirye-shiryen musayar fasaha, haɗa makamashi mai sabuntawa, amfani da fasahar ajiyar makamashi ta batir, fasahohin zamani na tsarin wutar lantarki, bincike, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma zuba jari su ne manyan fannonin da Kanada da NISO za su iya yin haɗin gwiwa a kansu.

A nasa jawabin, Babban Kwamishinan Kanada a Najeriya, David Sproule, ya tabbatar da aniyar ƙasarsa na tallafa wa Najeriya wajen sauya tsarin makamashi da kuma zamanantar da fannin wutar lantarki, ta hanyar amfani da ƙwarewar Kanada a fannonin gudanar da tsarin wutar lantarki, haɗa makamashi mai sabuntawa, fasahar ajiyar makamashi, tsaron yanar gizo da kuma gudanar da kasuwar wutar lantarki.